PSV Eindhoven ta lashe kofin Holland

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Kofi na 23 jumulla da PSV Eindhoven ta dauka a gasar Netherland

PSV Eindhoven ta dauki kofin gasar kwallon kafa ta Netherland, bayan da ta doke PEC Zwolle da ci 3-1 a wasan karshe na gasar bana da suka yi ranar Lahadi.

Kafin wasan karshen Ajax da PSV Eindhoven suna da maki iri daya, kuma Ajax ce ke kan gaba da yawan cin kwallaye shida a teburin gasar.

A wasan karshe na gasar da aka yi a ranar Lahadi Ajax ta tashi kunnen doki ne 1-1 da De Graafschap.

Hakan ya sa PSV ta hada maki 84 daga wasanni 34 da ta fafata a gasar, inda Ajax ta kammala da makinta 82.

PSV wadda aka ci wasanni biyu kacal dai dai da Ajax ta ci karawa 26 ta yi canjaras 6 ta kuma ci kwallaye 88 aka zura mata 32 a raga, inda ta lashe kofin gasar kasar karo na 23 jumulla.