Murray ya raba gari da kociyarsa Mauresmo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murray ya sha kashi a hannun Djokovic a gasar da aka yi a Spaniya

Dan kwallon tennis din Burtaniya, Andy Murray, ya raba gari da shi da mai horar da shi wasan, Amelie Mauresmo.

Murray mai shekara 28 ya yi aiki tare da Mauresmo tsawon shekara biyu, inda a tsakaninsu suka amince kowa ya kama gabansa.

Tun lokacin da Mauresmo ta fara horar da Murray kwallon tennis a Yunin 2014, ya lashe kofuna bakwai ciki har da guda biyu da ya ci a wasan turbaya.

Sai dai kuma dan wasan ya kasa lashe manyan kofuna a gasar ta tennis.

Murray wanda ya sha kashi a hannun Novak Djokovic a wasan karshe a Madrid ranar Lahadi, ya ci kofin US Open a 2012 da kuma na Wimbledon karkashin koci Ivan Lendl.