Ya kamata mu lashe La Liga ta bana - Enrique

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar za a buga wasannin karshe na gasar La Liga ta bana

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce ya kamata su dauki kofin gasar La Liga ta Spaniya ta bana, kuma na shida a cikin shekara takwas.

Barca wadda ke mataki na daya a kan teburi da maki 88, za ta iya lashe kofin bana idan ta doke Granada a ranar Asabar a wasan karshe na gasar.

Real Madrid ce ke matsayi na biyu da maki 87, za kuma ta ziyarci Deportivo La Coruna a wasan karshen mako na 38 a ranar ta Asabar.

A ranar Lahadi ne Barcelona ta doke Espanyol da ci 5-0 a wasan mako na 37 da suka yi, yayin da Real Madrid ta ci Valencia 3-2.

Real Madrid ta dauki kofin La Liga sau 32, inda Barcelona ta lashe sau 23 sai Atletico Madrid da ta dauka sau 10 jumulla.