Ebola zai fafata da Mai Takwasara a Zaria

Image caption Ebola daga Kudu na bin Mai Takwasara daga Guramada kisa

An tsayar da ranar 13 ga watan Mayu domin fafatawa a damben gargajiya na kasa da za a yi a Zaria ta jihar Kaduna.

Cikin manyan wasannin da za a yi har da wanda Mai Takwasara zai nemi fansar kisa a hannun Ebola.

A cikin watan Fabrairu Ebola ya buge Mai Takwasara a turmi na biyu a zaria a lokacin ajon Anas Dan Sarkin fawa.

A kuma cikin watan Afirilu 'yan damben biyu suka kara kwafsawa a jihar Sokoto inda suka tashi wasan canjaras a turmi biyu da suka taka.

Sun kuma hadu a jihar Kano da Legas a cikin watan na Afirilu kuma dukkan wasannin da suka yi babu kisa.

Ebola dan wasan Kudu da Mai Takwasara daga Guramada sune 'yan wasan damben gargajiya da suke tashe a wannan lokacin.

Kafin haduwar da suka yi a Zaria a cikin watan Fabarairu, sai da kowannensu ya yi wasa sama da shekara daya bai je kasa ba.