Indonesia na son daukar Mourinho

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Disamba Chelsea ta sallami Mourinho daga aiki

Indonesia na son daukar Jose Mourinho a matsayin kociyan tawagar kwallon kafar kasar in ji ministan wasannin kasar.

Indonesia wadda ke matsayi na 185 a matakin wadanda suka fi yin fice a murza leda a duniya an dakatar da ita daga shiga harkokin tamaula a bara, saboda katsalandan daga gwamnati.

Ministan wasannin kasar, Imam Nahrawi, ya ce ya tattauna kan batun dauko Mourinho da shugaban kasar, Joko Widodo kan cewar za su bashi albashin fan miliyan 13 a shekara.

Sai dai kuma Mourinho wanda Chelsea ta sallama daga aiki a Disamba, ana alakantashi cewar zai koma aikin horar da Manchester United.

Louis van Gaal ne ke jagorantar Manchester United kuma saura shekara daya yarjejeniyar da ya saka hannu a Old Trafford ta kare.