Liverpool za ta kara da Chelsea a Premier

Image caption Liverpool tana mataki na takwas a kan teburi, yayin da Chelsea ke matsayi na tara

Chelsea za ta ziyarci Anfield domin karawa da Liverpool a kwantan gasar Premier a ranar Laraba.

A wasan farko da suka yi a gasar a ranar 31 ga watan Oktoba Liverpool ce ta ci Chelsea 3-1 a Stamford Bridge.

Liverpool tana mataki na takwas a kan teburin Premier da maki 58, yayin da Chelsea ta hada maki 48 a matsayi na tara a teburin.

Sunderland ma za ta karbi bakuncin Everton a kwantan wasan mako na 30 a ranar Laraba.

Ita kuwa Watford za ta ziyarci Norwich a kwantan wasan mako na 35 a gasar ta Premier.