Welbeck zai yi jinyar watanni tara

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Arsenal tana mataki na uku a kan teburin Premier bana

Dan wasan Arsenal, Danny Welbeck, zai yi jinyar watanni tara, sakamakon aiki da likitoci suka yi masa a gwiwarsa.

Welbeck mai shekara 25, ya ji rauni ne a karawar da Manchester City ta tashi 2-2 da Arsenal a gasar Premier ranar Lahadi.

Hakan na nufin dan kwallon ba zai buga wa tawagar Ingila gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faranasa a bana, ba.

Tun bayan da aka tashi wasa a Ettihad, kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce ya damu da lafiyar Welbeck.

A cikin watan Fabrairu Welbeck ya dawo wasa, bayan da ya yi rauni a cikin watan Mayun 2015.