'Za mu dawo da martabar damben gargajiya'

Image caption Kwanaki uku za a yi wasan damben gargajiya na kasa a Kaduna daga ranar 13 ga watan Mayu

Shugaban kungiyar damben gargajiya ta Nigeria, Ali Zuma, ya ce za su dawo da martabar wasan a duniya.

Ali Zuma ya ce daya daga cikin matakan da suka dauka shi ne yi wa kungiyar rijista domin gwamnati ta san da zamansu.

Ya kuma kara da cewar suna gudanar da wasannin damben gargajiya akai-akai, inda suke gabatar da shi a jihohin kasa.

A ranar 13 ga watan Mayu za a gudanar da wasan damben gargajiya a birnin Zariya na jihar Kaduna.

Ali Zuma ya kuma ce da zarar kungiyar ta zauna da kafafunta, za su gayyaci masu ruwa da tsaki a wasan domin bayar da shawarar yadda za a ciyar da damben gargajiyar gaba.