Buffon ya tsawaita zamansa a Juventus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Juventus ce ta dauki kofin Serie A na bana kuma 5 a jere

Mai tsaron ragar Juventus, Ganluigi Buffon, ya tsawaita zamansa da kungiyar, har zuwa kakar 2018.

Buffon dan kasar Italiya ya koma murza-leda a Juve a shekarar 2001, ya kuma taimaka mata lashe kofin Serie A na biyar a jere a bana.

Shi ma mai tsaron bayan kungiyar, Andrea Barzagli, ya tsawaita yarjejeniyarsa zuwa shekarar 2018.

Barzagli wanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Italiya wasanni 54, zai yi ritayar yi wa kasar tamaula bayan gasar kofin nahiyar Turai ta bana.

Shi kuwa Buffon wanda ya yi wa Italiya wasanni 156, na fatan yin murabus daga buga wa kasar tamaula bayan kammala gasar cin kofin duniya ta 2018.