Liverpool da Chelsea sun buga 1-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool tana mataki na takwas Chelsea tana matsayi na tara a teburin gasar

Liverpool da Chelsea sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a kwantan wasan Premier da suka kara a ranar Laraba.

Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Hazard saura minti 13 a je hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma daf da za a tashi daga wasan Benteke ya farke wa Liverpool.

Saura wasa daya ya rage a kammala gasar bana, kuma Liverpool tana mataki na takwas a kan teburi da maki 59.

Chelsea kuwa tana matsayi na tara a teburin da maki 49.

Liverpool za ta ziyarci West Brom a wasan karshe na gasar a ranar Lahadi, yayin da Chelsea za ta karbi bakuncin Leicester City a ranar.