Keegan ya soki mai Newcastle da sakaci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Newcastle tana mataki na 18 a kan teburin Premier bana

Tsohon kociyan Newcastle United, Kevin Keegan ya soki mamallakin kungiyar da yin sakaci.

Newcastle United na daf da barin gasar Premier, bayan da take a mataki na 18 a kan teburin gasar da maki 34 kacal.

Kungiyar za ta buga wasan karshe na gasar bana da Tottenham a ranar Lahadi, sai dai kuma idan Sunderland ta ci kwantan wasanta da Everton, Newcastle sai dai ta tara a badi.

Keegan ya shaidawa BBC cewar mamallakin kungiyar Mike Ashley, ya dade yana yin kura-kurai da dama wajen yanke hukunci.

Ya kuma kara da cewa ya kamata su koma buga gasar Championship domin su sake daura damara.

Keegan ya ce Mike Ashley ne da laifi na kasa yin abin da ya dace, ko kuma wadanda ya bai wa damar yin hukunci ba su yi abinda ya dace ba.