Nasarawa United ta ci Abia Warriors 3-2

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na 16 a gasar Firimiyar Nigeria

Nasarawa United ta samu nasara a kan Abia Warriors da ci 3-2 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 16.

Abdulrahman Bashir ne ya fara ci wa Nasarawa kwallo a minti na 19 da fara wasa a karawar da suka yi a ranar Laraba.

Olaha ne ya farke wa Abia Warriors daf da za tafi hukun rabin lokaci.

Mintuna uku da dawo wa daga hutun ne, Emmanuel Makama ya ci wa Nasarawa kwallo na biyu a bugun fenariti.

Sai dai kuma ba a dauki lokaci mai tsawo ba Ndifreke Effiong ya farke wa Abia kwallon da aka zura mata.

Saura minti 17 a tashi daga karawar Abdulrahman Bashir ya ci kwallo na biyu a wasan kuma ta uku da Nasarawa United ta zura wa Abia Warriors.

Ga auran sakamakon wasannin da aka yi:
  • Ikorodu Utd 2-2 Plateau Utd
  • MFM 0-0 Enyimba
  • Sunshine Stars 2-1 Rangers
  • Shooting Stars 1-2 Wolves
  • Rivers Utd 1-0 Wikki
  • Nasarawa Utd 3-2 Abia Warriors
  • Ifeanyiubah 1-0 Lobi
  • Tornadoes 2-1 Heartland