Everton ta kori Roberto Martinez

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kociyan Everton, Roberto Martinez

Kungiyar Everton ta kori kociyanta, Roberto Martinez, bayan kwashe shekara uku yana horas da 'yan wasan kulob din.

A ranar Asabar ne Leicester ta lallasa Everton da ci 3-1 sannan kuma Sunderland ta casa ta da ci 3-0, ranar Laraba.

Everton ce ta 12 a teburin gasar Premier Ingila.

Kuma kungiyar ba ta yi nasara ba a wasan dab da na karshe na gasar FA Cup da ma League Cup, duka a wannan kakar wasanni.

Ana sa ran kulob din zai fitar da sanarwa a hukumance domin tabbatar da hukuncin korar Martinez.