Tennis: Dominick Thiem ya doke Federer

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Roger Federer bai ji dadin karo da Dominick Thiem ba

Dan wasan Tennis mai matsayi na 15 a duniya, Dominick Thiem ya doke Roger Federer, a gasar Italian Open.

Roger wanda ke fama da raunin da samu a bayansa, ya yi rashin nasara a zagaye na uku na wasan da suka buga, a inda aka tashi 7-6(7-2) da 6-4.

Federer wanda ya dauki kofin tennis na gasar har sau 17, ya yi kuskure sau 34 a wasan da ya yi a birnin Rome, kafin gasar French Open da za a yi ranar 22 ga Mayu.

Thiem, dan kasar Austria, mai shekara 22, zai fafata da Kei Nishikori a wasan dab da na karshe.