'Ina nan sai kwantiragi na ya kare'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ana sa ran shugaban Southampton Ronald Koeman zai karashe kwantiraginsa da kulob din, duk da ana danganta shi da gurbin manajan da ake da shi a Everton.

Dan asalin kasar ta Holland mai shekaru 53, ya fara aiki da Southampton ne a shekarar 2014, kuma sai a shekarar 2017 kwantaraginsa zai kare.

Da aka tambaye shi ko yana sa ran zai ci gaba da zama a Southampton din, Koeman ya amsa da cewa "eh" a wani taron manema labarai.

Ya ce, "Ni ne kociyan Southampton, kuma duk an sani cewa kwantiragin nawa da sauran shekara daya."