Barcelona ta dauki kofin La Liga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luis Suarez ne ya ci wa Barcelona kwallo uku a wasan da suka buga da Real Madrid

Kungiyar Barcelona ta lashe kofin gasar La Liga ta Spaniya, bayan da ta doke Kungiyar Granada da ci 3-0, a wasan karshe da suka yi ranar Asabar.

Dan wasan Barcelona, Luis Suarez ne dai ya jefa kwallayen uku baki daya a ragar ta Granada.

Yanzu Suarez ne ya lashe kyautar dan wasan da yafi kowanne yawan zura kwallaye.

Luis dai ya jefa kwallaye 40 a wannan kakar wasannin.

Wannan dai shi ne Karo na biyu a Jere da Barcelona take lashe wannan kofin.