An fara damben gargajiya na kasa a Zaria

Image caption An fara wasan damben gargajiya na kaa a Zariya

Kungiyar damben gargajiya ta Nigeria ta bude wasan dambe na kasa a birnin Zariya ta jihar Kaduna da safiyar Asabar.

Ali Zuma shugaban kungiyar damben ta Nigeria, ya ce makasudin yin wadannan wasannin bai wuce kokarin da suke na ganin sun dawo da martabar wasan a idon duniya.

Ya kuma ce daya daga cikin hanyar da za su raya wasan bai wuce su dinga gudanar da shi a jihohin kasar a lokaci zuwa lokaci.

A watan jiya ne aka gabatar da wasan a jihar Sokoko, bayan karamar sallah ake sa ran gudanar da wani damben kasa a Abuja.

Cikin wasannin da aka yi da safe an fafata a karawar matasan 'yan dambe, inda aka yi gumurzu tsakanin Dogon Shagon Tuwo da Ali Kwara kuma turmi uku suka yi babu kisa.

An kuma fafata tsakanin Bahagon Falgore da Shagon Shamsu, kuma turmi biyu suka taka babu kisa aka raba su.

Za a kamala wasannin Zariya a ranar Lahadi, inda ake sa ran yin gumurzu safe da yammaci, kuma a lokacin ne ake sa ran Ebola da Mai Takwasara za su kara a ranar..