An gayyaci Rashford cikin tawagar Ingila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marcus Rashford dan wasan Manchester United ne.

Kociyan Ingila, Roy Hodgson, ya saka sunan Marcus Rashford na Manchester United cikin 'yan wasan kwallon kafa na Ingila 26 da ya gayyata.

Cikin 'yan wasan da aka bayyana ne, za a fitar da guda 23 da za su wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai da za ayi a bana.

Dan wasan Newcaswtle United, Andros Townsend da na Arsenal, Jack Wilshere suna daga cikin 'yan wasan da aka gayyata.

Sai dai kuma babu sunan 'yan wasa Theo Walcott da Phil Jagielka da Jermain Defoe da kuma Mark Noble da Hodgson ya sanar.

Ranar 31 ga watan Mayu, Ingila za ta sanar da 'yan wasa 23 da za su buga mata gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a bana.

Ga jerin 'yan wasa 26 da aka fitar:

Masu tsaron raga: Joe Hart (Manchester City), Fraser Forster (Southampton), Tom Heaton (Burnley).

Masu tsaron baya: Gary Cahill (Chelsea), Chris Smalling (Manchester United), John Stones (Everton), Kyle Walker (Tottenham Hotspur), Ryan Bertrand (Southampton), Danny Rose (Tottenham Hotspur), Nathaniel Clyne (Liverpool).

Masu wasan tsakiya: Dele Alli (Tottenham Hotspur), Ross Barkley (Everton), Fabian Delph (Manchester City), Eric Dier (Tottenham Hotspur), Danny Drinkwater (Leicester City), Jordan Henderson (Liverpool), Adam Lallana (Liverpool), James Milner (Liverpool), Raheem Sterling (Manchester City), Andros Townsend (Newcastle United), Jack Wilshere (Arsenal).

Masu cin kwallo: Wayne Rooney (Manchester United), Harry Kane (Tottenham Hotspur), Jamie Vardy (Leicester City), Daniel Sturridge (Liverpool), Marcus Rashford (Manchester United).