An wanke Conte kan cogen haɗa wasa

Image caption An zargi Conte da kin ɗaukar mataki a lokacin da ake cogen haɗa wani wasa a 2011

An wanke zaɓaɓɓen kocin Chelsea Antonio Conte, daga duk wani laifi da ake tuhumarsa da shi na cogen haɗa wasa daga shekarar 2011.

Ana zargin kocin mai shekara 46 wanda zai jagoranci Italiya a gasar Euro ta 2016 a watan Yuni, da rashin ɗaukar mataki a lokacin da ake cogen haɗa wani wasa, yayin da yake jagorantar kungiyar Siena ta Italiya.

Sai dai wani alƙali a Cremona ya wanke Conte saboda rashin hujja kan zargin da ake masa.

Conte, wanda ya fuskanci haramcin shiga wasu al'amuran wasa da ke da alaƙa da wancan laifin a shekarar 2012, yanzu zai ja ragamar Chelsea bayan kammala gasar Euro.