Anichebe zai bar West Bromwich a bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Anichebe bai ci kwallo ba a bana a wasannin da ya yi wa West Brom

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Victor Anichebe, zai bar West Bromwich a watan gobe, bayan da kwantiraginsa ya kare.

Anichebe mai shekara 28, wanda ya koma West Brom daga Everton a Satumbar 2013, ya yi wasanni 63 ya kuma ci kwallaye tara.

Sai dai kuma wasanni uku aka fara wasa da shi a gasar Premier a bana, wadda aka kammala a ranar Lahadi.

Anichebe bai zura kwallo a raga ba a kakar wasan bana, bayan da ya yi wa West Brom wasanni daban-daban guda 14.