Schweinsteiger na cikin tawagar Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Schweinsteiger dan wasan Manchester United na yin jinya

Bastian Schweinsteiger yana cikin 'yan wasa 27 da tawagar kwallon kafa ta Jamus ta fitar na kwarya-kwarya.

Kocin Jamus, Joachim Low, ya bayyana Schweinsteiger, a matsayin kyaftin din tawagar duk da cewa rabon da ya buga wa Jamus tamaula tun a cikin watan Maris.

Schweinsteiger ya yi rauni ne a lokacin da yake yi wa Jamus wasa, inda yanzu haka yake yin jinya bayan da likitoci suka yi masa aiki.

Cikin sunayen da Jamus ta fitar, za ta bayyana 'yan wasa 23 a ranar 31 ga watan Mayu, wadanda za su wakilceta a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Jamus tana rukuni na uku da ya kunshi Ireland ta Arewa da Poland da kuma Ukraine.