Ana taro kan Syria a Geneva

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yaki ya kassara garuruwa da birane a Syria

Kasashe masu karfin fada a ji a duniya da na gabas ta tsakiya sun fara tattaunawa kan yadda za a cigaba da batun dakatar da yaki a Syria.

Ana sa ran cewa taron wanda da ake yi a Vienna bisa jagorancin Amurka da Rasha, zai mayar da hankali kan shirin tsagaita wuta da kuma bude hanyoyin kai agajin gaggawa.

Ministan kasashen waje na Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya ce yana kyautata zaton cewa tattaunawar za ta bude kofar dawowar sulhu tsakanin bangaren gwamnati da 'yan adawa.

A watan da ya gabata ne dai shirin cimma zaman lafiya tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa, ya ci tura sakamakon fitar da 'yan adawa suka yi daga taron tattaunawar a Geneva.