An sayar da Aston Villa fan miliyan 60

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston Villa za ta koma buga gasar Championship a badi

Fitaccen dan kasuwar China, Dr Tony Xia, ya amince zai sayi kungiyar Aston Villa kan kudi fan miliyan 60.

Za a kammala yarjejeniyar sayar da Villa idan hukumar kwallon kafa ta Ingila ta amince da cinikin.

Mamallakin kungiyar Randy Lerner ne ya sa kungiyar a kasuwa a shekarar 2014, wadda ya saya kan kudi sama da fan miliyan 62 a shekarar 2006.

Ba za kuma a sanar da wanda zai horar da kungiyar ba tsakanin Nigel Pearson da Roberto di Matteo ba har sai an kammala cinikin.

Villa za ta buga gasar Championship a badi, bayan da ta fadi daga gasar Premier bana.

Kungiyar ta kammala gasar Premier a mataki na 20 da maki 17 kacal.