Wasanni 49 Barcelona ta ci a bana

Image caption Barcelona ce ta dauki kofin La Liga na bana na biyu a jere

Barcelona ta lashe wasanni 44 a dukkan fafatawar da ta buga a kakar kwallon kafa ta bana.

Barcelona ta yi wasan farko a bana ranar 11 ga watan Agustan 2015 a gasar UEFA Super Cup da Seville, inda ta lashe kofin da ci 5-4 bayan da suka tashi karawar 4-4.

Haka kuma kungiyar ta Spaniya ta yi canjaras a karawa tara sannan aka ci ta wasanni bakwai.

A kakar bana ne Barcelona ta kafa tarihin yin wasanni 39 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan karawar da ta yi.

Kungiyar ce ta lashe kofin La Liga na bana na biyu a jere na kuma 24 jumulla.

Kuma Luis Suarez ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar ta Spaniya, inda ya zura 40 a raga.

Barcelona wadda aka fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai a wasan daf da na kusa da karshe, za ta yi wasan karshe a Copa del Rey da Seville ranar 22 ga watan Mayun nan.