Nasarawa United ta ci Lobi Stars 2-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na 18 da aka yi a gasar Firimiyar Nigeria

Nasarawa United ta doke Lobi Stars da ci 2-1 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 18 da suka yi a ranar Laraba.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi, Sunshine Stars ta ci Wikki Tourist 3-1, yayin da Ikorodu ta doke Warri Wolves 1-0.

Shooting Stars kuwa 2-0 ta ci Abia Warriors, Rivers United ta hada maki uku bayan da ci Akwa United daya mai ban haushi, sai Heartland da Plateau United da suka tashi canjaras.

Sai a ranar Alhamis za a yi gumurzu tsakanin IfeanyiUbah da MFM da kuma fafatawa tsakanin Niger Tornadoes da Kano Pillars.

Ga sakamakon wasannin da aka yi:
  • Rivers Utd 1-0 Akwa Utd
  • Ikorodu Utd 1-0 Wolves
  • Nasarawa Utd 2-1 Lobi
  • Heartland 0-0 Plateau Utd
  • Sunshine Stars 3-1 Wikki
  • Shooting Stars 2-0 Abia Warriors