Sevilla ta lashe kofin Europa na hudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sevilla za ta kara da Barcelona a Copa del Rey a ranar 22 ga watan Mayu

Sevilla ta dauki kofin Zakarun Turai na Europa na bana, bayan da ta doke Liverpool da ci 3-1 a karawar da suka yi a Basel.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Daniel Sturridge ana saura minti 10 a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne Kevin Gameiro ya ci wa Sevilla kwallo, kuma Andujar Moreno ya ci ta biyu ya kuma kara ta uku.

Da wannan nasarar da Sevilla ta yi za ta buga gasar cin kofin Zakaru ta Champions League ta badi kai tsaye.

Kungiyar ta Spaniya ta lashe kofin Europa sau biyu kenan a jere wannan ne kuma karo na hudu da ta lashe kofin.

Sevilla za kuma ta buga wasan karshe na Copa del Rey da Barcelona a ranar 22 ga watan Mayu.

Liverpool ta kare gasar Premier bana a mataki na takwas a kan teburi da maki 60.