Aston Villa za ta kashe £50m domin farfadowa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai kulob din Aston Villa, Dr Tony Xia

Mutumin da ya sayi Aston Villa, Dr Tony Xia ya ce zai ba wa duk wanda ya zamo sabon kociyan kungiyar £50m wajen sake daukaka darajar kulob din domin komawa gasar Premier.

Dr Xia ya kuma tabbatar da cewa tsohon kociyan Chelsea da West Brom, Roberto di Matteo, yana daga cikin 'yan takarar neman horas da kulob din.

A wannan makon ne dai Tony Xia ya sayi Aston Villa daga wurin Randy Lerner, a kan kudi £60m, bayan da hukumar gasar League ta amince da cinikin.

Aston Villa ce dai kurar baya a gasar Premier Ingila ta bana kuma yanzu haka za ta koma buga wasa a matakin na biyu na wasan kwallon kafa a Ingila, a karon farkon tun 1988.