Abin da zai sa Benitez ya tsaya a Newcastle

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Maris ne Benitez ya maye gurbin Steve McClaren

Abin da zai sa kociyan Newcastle United, Rafael Benitez, ya cigaba da zama a kulob din shi ne irin yawan kudin da za a zuba domin tayar da komadar kungiyar.

A watan Maris ne dai Benitez ya karbi jagorancin kulob din amma hakan bai hana kungiyar fita daga gasar Premier ba, duk kuwa da cewa Newcastle din ta yi nasarar wasannin uku, a wasanninta shida.

Yanzu haka an ce Benitez ya tattauna da shugabannin kulob din kuma ana kyautata zaton tattaunawar za ta yi nasara.

Newcastle United ya gama gasar Premier a mataki na 19.