Tennis: Federer ya fita daga French Open

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer ba zai buga wasan French Open ba

Dan wasan tennis wanda a baya ya rike matsayi na daya, Roger Federer, ya fita daga gasar French Open, sakamakon ciwon da ya samu a bayansa.

Dan wasan mai shekara 34 bai buga wasan da aka yi a gasar Madrid Open ba da aka yi a farkon watannan, saboda raunin da ya ji a bayansa a lokacin yana wasan gwaji.

Federer ya ce "ina samun sauki amma ba dari bisa dari ba."

Wannan ne karon farko da Federer ba zai buga wasa ba a gasar kwallon tennis.