Na dauki alhakin rashin nasararmu — Klopp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya dauki alhakin rashin nasarar da kulob din nasa ya yi, a lokacin wasan karshe na gasar Europa da suka buga da Sevilla, a inda aka tashi 3-1.

Jurgen ya ce kulob din zai dage wajen dawo da martabarsa.

Rashin nasarar dai tana nufin Liverpool din ba za ta buga wata gasa ta turai ba a kakar wasa mai kamawa.

Klopp ya ce "na dauki alhakin abin da ya faru. Amma na yi wa kowa alkawari cewa za mu yi amfani da wannan damar wajen kara kaimi, a nan gaba."