'Za a iya haramtawa Sharapova wasa'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lokacin da Maria Sharapova take yin bayani kan shan kwayar meldonium.

Shugaban hukumar kwallon tennis ta Rasha, Shamil Tarpishchev, ya ce maiyiwuwa ne 'yar wasan tennis 'yar Rasha, Maria Sharapova ba za ta sake buga wasa ba har abada.

A watan Janairu ne dai aka gano Sharapova, mai shekara 29, tana shan kwayar meldonium, a lokacin gasar Australian Open.

Tarpishchev ya ce "yana tantama" idan za a kyale Sharapova ta sake buga wani wasa a nan gaba.

Daman dai Hukumar Kwallon Tennis ta Duniya, ITF, ta dakatar da Maria, a watan Maris.

Yanzu haka, Sharapova tana jiran hukuncin da za a yanke mata wanda zai iya zama haramci na shekara hudu.

Sai dai wasu masana na ganin hukuncin zai iya zama dakatarwa ta watanni shida zuwa 12.