Za mu ci gaba da daukar kofuna — Mata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata ya ce Manchester United zai dawo kan ganiyarsa.

Dan wasan tsakiya na Manchester United Juan Mata ya ce yana da yakinin cewa kulob din zai dawo kan ganiyarsa ta daukar kofuna a watanni 12 masu zuwa saboda azamarsa.

Manchester United bai dauki manyan kofuna ba tun da kociya Sir Alex Ferguson ya yi ritaya daga harkokin kwallon kafa a shekarar 2013.

Sai dai kuma kulob din - wanda ya kare a mataki na biyar a saman tebirin gasar Premier - zai iya daukar kofin FA idan ya doke Crystal Palace ranar Asabar.

Mata ya shaida wa BBC Sport cewa,"Wannan kulob din zai dawo da daukar kofuna. Manchester United na dab da daukar wani kofin, kuma muna da azamar daukarsa. Don haka na tabbatar cewa za mu dawo ganiyarmu ta daukar kofuna."

Mata ya amince cewa abin kunya ne a gare su da suka kasa samun gurbin buga gasar zakarun turai a kakar wasa mai zuwa, yana mai cewa yana da kwarin gwiwa cewa za su dawo kan ganiyarsu.