Moukandjo ba zai yi wa Kamaru wasa ba

Hakkin mallakar hoto Matwew Lewis Getty
Image caption Kamaru za ta fafata da Faransa a ranar 30 ga watan Mayu

Benjamin Moukandjo ba zai buga wa Kamaru wasan sada zumunta da za ta yi da Faransa ba, sakamakon raunin da ya yi.

Hukumar kwallon kafa ta Kamaru ta sanar da cewar Mbilla Etame, mai taka leda a Antalyasport ne zai maye gurbinsa.

Shi ma kyaftin din Kamaru, Stephane Mbia, ba ya cikin jerin 'yan wasa 24 da kocin tawagar kasar Hugo Broos ya sanar.

Mbia mai shekara 29, ba zai kuma buga fafatawar da Kamaru za ta yi da Mauritania ranar 3 ga watan Yuni a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ba.

Su ma Sebastien Bassong mai taka-leda a Norwich City da Marvin Matip da kuma Landry N'guemo ba sa cikin 'yan wasan da aka gayyata.

Sai dai kuma an bai wa Clinton Njie na Tottenham goron gayyata da kuma 'yan wasan da suke murza-leda a gida, da suka hada da Mohammed Djete na Union Douala, da Aaron Mbimbe na Coton Sports da kuma Jonathan Ngwem na Unisport.

Ga jerin 'yan wasa 24 da Kamaru ta bai wa goron gayyata:

Masu tsaron raga: Andre Onan (Ajax, Netherlands), Guy Roland Ndy Assembe (Nancy, France), Fabrice Ondoa (Tarragona, Spain)

Masu tsaron baya: Allan Nyom (Watford, England), Nicoals Nkoulou (Marseille, France), Aurelien Chedjou (Galatasaray, Turkey) Henri Bedimo (Lyon, France) Ambroise Oyongo (Montreal Impact, MLS) Adolphe Teiku (Sochaux, France) Jonathan Ngwem (Unisport Bafang), Mohammed Djettei (Union Douala) Aaron Mbimbe (Coton Sport Garoua)

Masu wasan tsakiya: Franck Kom (Etoile du Sahel, Tunisia), Eyong Enoh (Standard Liege, Belgium) Georges Mandjeck (Metz, France) Sebastien Siani (KV Oostende, Belgium)

Masu zura kwallo: Vincent Aboubakar (FC Porto, Portugal), Eric-Maxime Choupo-Moting (Schalke, Germany), Mbilla Etame (Antalyasport, Turkey), Jacques Zoua (Ajaccio, France), Anatole Abang (New York Red Bulls, MLS) Karl Toko (Sochaux, France), Clinton Njie (Tottenham Hotspur, England), Edgar Sali (St Gallen, Switzerland)