Ba a gaya wa Van Gaal ya samu magaji ba

Image caption Manchester United ta dauki kofin kalubale na 12 jumulla

Ba a sanar da Louis van Gaal cewar Jose Mourinho ne zai maye gurbinsa a matsayin kociyan Manchester United ba.

BBC ta fahimci cewar karawar da Manchester United ta lashe kofin kalubalen da ta buga da Crystal Palace, shi ne wasan karshe da Van Gaal ya jagoranci United.

Haka kuma kocin da mataimakansa ba su san cewar mataimakin shugaban United Ed Woodward, ya riga ya kammala komai kan daukar Mourinho ba.

Lokacin da wani dan jarida ya nufi Van Gaal da tambaya a ranar Lahadi ya amsa masa da cewar an gama komai, yana kuma nufin kakar wasa ta kare ba makomar aikinsa ba.

Sauran ma'aikatan da suka taimaka wa Van Gaal da gudanar da aiki za su je yin hutu.

United ta kammala gasar Premier ta bana a mataki na biyar a kan teburi, za kuma ta buga kofin zakarun Turai na Europa, ta kuma dauki kofin FA na 12 jumulla.