Wikki Tourist ta doke Ikorodu da ci 3-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption An kammala wasannin mako na 19 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Wikki Tourists ta samu nasara a kan Ikorodu United da ci 3-0 a gasar Firimiyar Nigeria, wasan mako na 19 da suka kara a ranar Lahadi.

Hamza Tiya ne ya fara zura kwallo a raga a minti na 19 da fara wasa, Saidu Abdullahi shi ne ya ci ta biyu kafin hutun rabin lokaci ya kuma kara ta uku bayan da aka dawo daga hutu.

Sauran wasu sakamakon karawar mako na 19 Warri Wolves ta ci El-Kanemi Warriors 3-1, Lobi Stars ta ci Rivers United daya mai ban haushi.

Niger Tornadoes 2-0 aka doke ta a gidan IfeanyiUbah, sai Abia Warriors da ta yi rashin nasara a gida a hannun Sunshine Stars da ci 2-1.

Ga sakamakon wasannin mako na 19 da aka yi:
  • Plateau Utd 0-0 Pillars
  • Wolves 3-1 El-Kanemi
  • Wikki 3-0 Ikorodu Utd
  • Abia Warriors 1-2 Sunshine
  • Lobi 1-0 Rivers Utd
  • FC Ifeanyiubah 2-0 Tornadoes
  • Akwa Utd 2-0 Shooting Stars
  • Enyimba 1-0 Nasarawa Utd
  • Rangers 0-0 Heartland