Varane ba zai buga wasa da Atletico ba

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid ne a ranar 28 ga watan Mayu

Watakila dan kwallon Real Madrid, Raphael Varane ba zai yi wasa a karawar da kungiyar za ta yi da Atletico Madrid ba.

Real Madrid ce ta sanar da cewar Varane mai shekara 23, yana da rauni a kafarsa ta hagu, ba ta kuma sanar da ranar da zai gama yin jinya ba.

Sai dai kuma mujallun kasar Spaniya sun wallafa cewar dan kwallon ba zai buga wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai da za a yi a San Siro ba.

Haka kuma da kyar ne idan zai buga wa Faransa wasan farko da za ta yi a gasar cin kofin nahiyar Turai.

Faransa mai masaukin baki za ta fara wasan farko na bude gasar bana da Romania a ranar 10 ga watan Yuni.