Barcelona ta lashe Copa del Rey na Spaniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Barcelona ta lashe Copa del Rey na Spaniya na bana, bayan da ta doke Sevilla da ci 2-0.

Tun farko sun tashi karawar babu ci a mintuna casa'in da suka fafata.

Bayan da aka shiga karin lokaci ne Jordi Alba ya ci wa Barcelona kwallo, sannan Neymar Da Silva ya ci na biyu.

Barcelona wadda ta lashe kofin La Liga na bana ta dauki Copa del Rey sau 28 jimilla, ita kuwa Sevilla ita ce ta lashe kofin Europa bayan ta ci Liverpool 3-1.