UEFA ta tuhumi Liverpool da Sevilla

Sevilla ce ta lashe kofin, bayan da ta ci Liverpool 3-1
Bayanan hoto,

Sevilla ce ta lashe kofin, bayan da ta ci Liverpool 3-1

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai, UEFA, ta tuhumi Liverpool da Sevilla da tayar da hayaniya a wasan karshe na cin kofin Europa da suka yi.

Magoya bayan kungiyoyin biyu sun kwafsa kafin a fara karawar a filin wasa na St Jakob-Park da ke Basel, bayan da mabiya Liverpool suka sayi tikitin da bai raba wajen zama da magoya Sevilla ba.

Sevilla wadda ta lashe kofin da ci 3-1, ta sayar da tikitin kallon wasan guda 7,000 daga cikin 9, 000 da aka ware mata, dalilin da ya sa magoya bayan Liverpool suka mamaye ko ina a filin.

An kuma tuhumi magoya bayan Liverpool da kunna wuta mai tartsasti a lokacin fafatawar.

Ita kuwa Sevilla an tuhumi mabiyanta da jefa abubuwa cikin fili da sauran wurare da dama.

Sai a ranar 21 ga watan Yuli ne hukumar kwallon kafa ta Turai za ta saurari bahasin kungiyoyin biyu.