Kakar tamaular bana san barka - Enrique

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kofuna hudu Barcelona ta ci a kakar wasannin bana

Kociyan Barcelona, Luis Enrique, ya ce kakar kwallon kafa ta bana da suka fafata alasan barka.

Enrique ya ce sun taka rawar gani duk da kasa lashe kofin Zakarun Turai na bana da suka dauka a bara.

Atletico Madrid ce ta fitar da Barca daga gasar Zakatun Turai a wasan daf da na kusa da karshe.

Barcelona wadda ta lashe kofin La Liga na Spaniya na bana, ita ce ta dauki Copa del Rey bayan da ta ci Sevilla 2-0 a ranar Lahadi.

Kociyan ya ce sun yi kokari da suka dauki kofuna hudu daga cikin guda shida da aka yi gumurzun lashe wa a kakar wasannin bana.

Barcelona ta kuma dauki Uefa Super Cup da na Zakarun kungiyoyin nahiyoyi wato Fifa Club World Cup.