An kori Van Gaal daga Man Utd

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kori Van Gaal ne kafin cikar wa'adinsa.

Kulob din Manchester United ya kori kocinsa Louis van Gaal a daidai lokacin da ake sa ran tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho zai maye gurbinsa.

An kori Van Gaal ne bayan ya kammala shekara biyu cikin uku na kwantaraginsa.

Da ma dai BBC Sport ta ba da rahoton cewa wasan da kulob din United ya doke Crystal Palace na cin kofin FA shi ne na karshe da zai buga.

Ana sa ran tabbatar da nadin Mourinho idan ya gana da manyan jami'an United ranar Talata.

Har yanzu ba a san rawar da Ryan Giggs, mataimakin Van Gaal zai taka ba a karkashin Mourinho ko kuma abin da zai faru ga sauran mutanen da ke aiki da koci.