Ronaldo ya ji rauni a wajen atisaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ronaldo ya ci kwallaye 51 a kakar wasannin bana

A ranar Talata Cristiano Ronaldo ya kuje a cinyarsa, bayan da ya yi taho-mu-gama da mai tsaron ragar Real Madrid Kiko Casilla.

Ronaldo ya ce bai yi rauni ba zai kuma iya buga wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da Madrid za ta yi da Atletico Madrid a ranar Asabar.

Dan wasan tawagar Portugal ya ce ya dan bugu ya kuma kuje, amma zai murmure kafin ranar Asabar din.

Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid a wasan karshe a gasar zakarun Turai, maimaicin karawar da suka yi a 2014 a gasar, in da Real ta ci wasan 4-1.