Manchester United za ta dauki Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manchester United ta kori Van Gaal a ranar Litinin

Watakila Manchester United ta dauki Zlatan Ibrahimovic da zarar ta nada Jose Mourinho a matsayin sabon kociyanta.

Yarjejeniyar Ibrahimovic dan kasar Sweden mai shekara 34, ta kare da Paris St-Germain a karshen kakar wasa ta bana.

An yi wa dan kwallon tayin kwantiragi mai tsoka a China, bayan da wasu kungiyoyin Premier suka fara zawarcinsa.

Ibrahimovic ya yabi kwarewar Mourinho a fagen horar da tamaula da yadda ya samu kwarewa a karkashinsa a baya.

A ranar Talata ake sa ran Manchester United za ta nada Jose Mourinho a matsayin sabon kociyanta domin ya maye gurbin Louis van Gaal.