Valencia ta nada sabon koci

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Valencia ta kammala gasar La Ligar bana a mataki na 12 a kan teburi

Valencia ta nada Pako Ayestaran a matsayin sabon kociyanta, kan yarjejeniyar shekara biyu.

A watan Maris ne aka sanar da kocin wanda ya yi mataimaki a Liverpool, zai horar da Valaencia zuwa karshen kakar wasan bana,

Kocin mai shekara 53, ya kuma maye gurbin Gary Neville wanda ya jagoranci Valencia watanni hudu kacal.

Ayestaran ya jagoranci tsohuwar kungiyar tasa lashe wasanni uku daga cikin guda takwas, inda Valencia ta kare a mataki na 12 a kan teburi.

Kocin ya horar da Maccabi Tel Aviv tamaula, inda ya jagorance ta lashe kofin Isra'ila a shekarar 2015.