Ghaly zai koma wasa a tawagar Masar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masar za ta kara da Tanzaniya a cikin watan Yuni

Shugaban kungiyar Al Ahly, Mahmud Taher, yana goyon bayan Hossam Ghaly da ya koma buga wa tawagar Masar tamaula.

Tun farko, kyaftin din Al Ahly, Ghaly, ya yi cacar baki ne da mataimakin kociyan tawagar Masar, Osama Nabeh, a cikin watan Maris.

Hakan ne ya sa Ghaly ba ya cikin 'yan kwallon da Masar ta gayyata wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta kara da Tanzani a cikin watan Yuni.

Taher ya ce ya tattauna da Hany Abo Rida, jami'in da ke sa ido a kan tawagar Masar, sun kuma shawo kan matsalar tsakanin mataimakin kocin da dan wasan.

Tun farko an shirya yin tattaunawar tare da Ghaly da kuma Nabeh, amma sakamakon gasar kasar Masar da dan wasan zai yi bai sa sun gana ba.