Arsenal ta sayi Granit Xhaka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Xhaka zai koma Arsenal ne bayan kammala gasar Euro 2016.

Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta sayi dan wasan tsakiya na Switzerland Granit Xhaka daga Borussia Monchengladbach.

Dan wasan, mai shekara 23, wanda ya bugawa tawagar kasarsa wasa 41 sannan ya zama kyaftin din Jamus, ya sanya hannu kan kwantaragi ta lokaci mai tsawo a kungiyar, ko da ya ke ba a fadi kudin da za a biya shi ba.

Xhaka ya ce "Ina matukar alfaharin zuwa Arsenal. Na zaku na koma London, domin wakiltar wannan kungiya ta musamman, sanna na buga wasa a gasar Premier."

Dan wasan ya kara da cewa "Zan yi bakin kokari na domin ganin Arsenal ta lashe kofuna domin faranta ran masu goyon bayanta."

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce: "Granit Xhaka dan wasa ne mai kuzari, inda ya taka muhimmiyar rawa a gasar zakarun Turai da ta Bundesliga".

"We have been watching him for a long time now and he is a player who will add quality to our squad."

Xhaka, wanda ya zura kwallo shida a wasanni 108 da ya buga a gasar Bundesliga, zai koma Arsenal ne bayan kammala gasar Euro 2016, wacce za a fara daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yuli.