Jose Mourinho ne sabon kocin Man Utd

A hukumance, an tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin sabon kocin kungiyar Manchester United bayan ya saka hannu a kontiragin shekara uku.

Sabon kocin ya maye gurbin Louis Van Gaal, wanda aka sallama ranar Litinin, kwanaki biyu bayan kungiyar ya lashe kofin FA.

Mataimakin shugaban hukumar gudnarwar kungiyar, Ed Woodward, ya ce, "Babu kocin da ya kai Jose a fagen kwallon kafa a yau".

Mourinho, mai shekara 53, ya ce "A harkar kwallon kafa, kasancewa kocin Manchester United wata girmamawa ce ta musamman. Kulob ne da ya yi suna kuma mutane ke so a duniya."

Ya kara da cewa, "Na zaku na kama aiki a matsayin kocin kungiyar, kuma ina sa ran samun goyon bayansu a shekaru masu zuwa".