Reading ta kori kocinta Brian McDermott

Kungiyar kwallon kafa ta Reading ta kori kocinta, Brian McDermott, bayan wata biyar da nada shi.

Rahotanni daga Holland na cewa tsohon dan wasan kungiyar Manchester United, Jaap Stam, wanda a baya-bayan nan ya bar matsayinsa na koci a Ajax na neman aikin.

McDermott, mai shekaru 55, ya koma filin wasan Madejski ne a watan Disamba a karo na biyu a matsayin kocin kulob din Reading.

Ya ci wassani tara a cikin 30 da ya buga kuma yanzu kulob din shi ne na 17 a gasar League 2 ta Ingila.