Tottenham za ta koma Wembley

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Filin wasa na kasar Ingila

Tottenham ta cim ma yarjejeniya don buga wasanninta na gida a gasar zakarun Turai cikin filin Wembley a kaka mai zuwa.

Haka kuma, kungiyar tana da zabin buga duk wasanni da gasar cin kofuna na Ingila da na Turai a filin wasa na kasar a shekara ta 2017-2018.

Kulob din dai yana gina wani sabon filin wasa a kan kudi fam miliyan 400 a kusa da filin wasan kungiyar na yanzu White Hart Lane.

Tottenham na sa ran kammala aikin gina sabon filin ne a kan lokaci don bugawa wasannin kakar shekara ta 2018 zuwa 2019.