An ceto dan wasan Olympiakos Alan Pulido

Image caption An sace Mr Pulido ne bayan fitarsa daga wani wurin dabdala, a kusa da garinsu.

Jami'ai a Mexico sun ce an ceto Alan Pulido, dan kwallon kafar da aka sace a arewa maso gabashin kasar, ranar Lahadi.

An sace Mr Pulido, mai shekara 25 ne bayan fitarsa daga wani wurin dabdala, a kusa da garinsu Ciudad Victoria a jihar Tamaulipas.

Hukumomi sun ce babu abin da ya same shi.

Wasu hotuna da kafafen watsa labaran kasar suka fitar sun nuna shi sanye da bandeji a hannu.

Mr Pulido yana murza leda a kungiyar kwallon kafar Olympiakos da ke kasar Girka, kuma ya buga wa kasarsa ta Mexico kwallo da dama.

Barayi dai kan sace dubban mutane a Mexico a kowace shekara, kuma ana danganta barayin da mu'amala da miyagun kwayoyi.