Likitoci sun yi wa Ginola aiki ya koma gida

Hakkin mallakar hoto PA

David Ginola, tsohon dan kwallon Faransa ya koma gida, bayan da likitoci suka yi masa aiki, bayan da ya gamu da bugun zuciya.

Ginola mai shekara 49 tsohon dan kwallon Newcastle United da Tottenham ya gamu da ciwon bugun zuciya a lokacin da yake taka-leda a Kudancin Faransa a ranar Alhamis 19 ga watan Maris.

Tsohon dan wasan tawagar Faransa ya yi ritaya a cikin watan Mayun 2012, daga nan ne ya koma yin sharhin tamaula a BBC da BT Sports da Canal Plus da CNN.

Ginola, ya kuma buga wa Aston Villa da Everton wasannin kwallon kafa.